Majiyoyin kiwon lafiya a zirin Gaza sun sanar da cewa akalla mutane 70 ne suka yi shahada a cikin sa'o'i 24 da suka gabata sakamakon munanan hare-haren da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai kan yankunan mazauna wannan tsibiri.
A bisa wannan rahoton 45 daga cikin wadannan shahidai sun kasance mazauna a arewacin zirin Gaza.